[...] “Ina da shawara.” Ya jingina gaba kamar yadda abokiyata Afrilu ke yi lokacin da take son faɗan wani sirri, duk da cewar babu wani sirrinta da ke wani amfani. Ko a ce ma sirri ne da gaske. “Idan baka gaya wa kowa ina nan ba, zan iya gyara idanuwanka.”
“Bar garin!”
Ya lumshe sau da dama. "Abin da nake ƙoƙarin yi ke nan.”
“Abin da nake nufi shine ba za ka iya yin hakan ba!"
“Me ya hana?"
"To, babu wanda ya taɓa iya gyara idanuwana, banda gilashin."
“Ina da wasu baiwa. Za ka gani, muddin...”
“…Ban gaya wa kowa game da kai ba?”
“Wannan shine ainihin batun, shine zancen.”
“Ta yaya zan san ba za ka maƙantar da ni ba? Kana iya zama kamar ɗaya daga cikin waɗancan masu tallan kan-layi suna yin alƙawura amma gabaɗaya ƙarya ne.”
Maimaicin ya fara kuma. “Ba zan yi irin wannan abu ga wani halitta da bai cutar da ni ba."
“Ma'ana idan na cutar da kai, za ka iya sa ni in maƙanta?”
“Wannan akan buƙatar neman-sani ne.”
“Kuma idan ka gyara idanuwana, kuma ban gaya wa kowa game da kai ba, za ka bar gonakinmu?”
“Wannan shine ainihin batun!” [...]