[… Franklin Bulls ke riƙe da ƙwallo a halin yanzu kuma kai-tsaye Payton Hughes sun sami ƙwallo kuma sun miƙa ta zuwa Kendry Rams wanda ke neman kutsawa cikin hanzari sannan tsaye a wurin wani matashi ne mai jini a jika wato Tom Isaac wanda shi wannan Tom Isaac kwata-kwata kamar babu mai tsaronsa a cikin wannan wasa kamar yana jiran wata dama ce ta zo kamar dai babu wanda yake tsare shi kawai dai suna wani salon wasa ne wanda zai ba su damar zura ƙwallo, kawai dai sun bar shi a gefe domin samun dama ta samun nasara to amma su kuma Bulls sun gane wannan wayon saboda haka basu ba da wata dama ba ta barin samun nasara ta amfani da wannan salo. E Isaac, wannan hange ne mai kyau domin bakiɗayan wannan salo na tsaro ya tattara ne a wannan ɓangaren filin wasan inda yake sa ran cin ƙwallo ɗaya mai maki uku ta hanyar jifan haɗa baya-da-baya wanda zai yi wahala ya sami haka. To amma Martin kana jin cewa su ma za su sami damar kai wa zuwa bakin raga? Dama ta biyu ta sake samuwa ga Rams wanda kamar ba ya cikin wasan. Ban taɓa ganin abun ban sha’awa irin wannan ba daga Rams a wasan ƙwallon Kwando. Abun akwai burgewa …]